Alamomi sunfara nuna cewa an fara samun cigaba akan yaki da cutar COVID19 a kasar sin inda bayanai suka nuna ba a kara samun wanda ya kara kamuwa da cutar ba.

Hedikwatar cutar Corona Covid19 wato birnin sin, rahotanni sun bayyana an fara samun cigaba kan yaki da cutar Corona wadda ta addabi duniya baki daya, bisa ga rahoton da kasar ta fitar a yau ya nuna an samu cigaba sosai wajan dakile wannan Annoba inda hukumar lafiya dake kasar sin suka bayyana da cewa har zuwa yanzu ba a samu wanda ya kara kamuwa da cutar ba a dukka fadin kasar.

Sai dai a cewar hukumar akwai sabbin rahotanni kusan 36 wadanda sun shigo ne daga kasashan waje, da cutar kasar.

Rahotanni ya bayyana adadain wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 80,967, wadanda kuma suka mutu a sakamakon cutar ya kai 3,248, sannan adadain wanda suka warke daga cutar sun kai 71,150.

Daman masu iya magana sunce dan hakin da kake rainawa shi zai tsonema ido.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top