Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya dauki hotunan fashewar iskar gas wanda ya yi sanadin rayuka 20 a cikin jihar ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a Abuja.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani sako da yayi a ranar Litinin.
Ban da mutane 20 da suka mutu a fashewar da ta faru a yankin Abule Ado da ke Legas a ranar Lahadin da ta gabata, an kuma samu jikkatar mutane da dama tare da asarar dokiyoyi.
Kafin ganawa da Buhari, Sanwo-Olu ya ware biliyan biyu a ranar Litinin domin taimakawa wadanda ibtila’in ya shafa tare da yin kira ga mambobin jama’a da su bayar da gudummawar su.
Ya kuma ba da sanarwar kafa “Asusun bada taimakon gaggawa na Abule Ado” bayan ya ziyarci wurin da fashewar ta afku.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment