Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin ta dakatar da wasu mambobin majalisar biyar saboda zargin su da keta dokokin majalisar.
Kakakin majalisar Abdulazeez Gafasa, wanda ya ba da sanarwar dakatar da su a yayin wani zama da majalisar tayi, kakakin majalisar ya zargi ‘yan majalisar da jagorantar tada tarzoma da tarwatsa zaman majalisar da ya gabata a wancan makon.
Idan zaku iya tunawa a wancan zaman wasu yan majalisu sun nemi tarwatsa zaman, akan rahotan tuhuma da ake shirin gabatarwa akan tsohon sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.
Yan majalisar da abin ya shafa sun hada da mambobi uku na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da biyu na jam’iyyar Democratic Party (PDP).
© Abubakar Saddiq
Post a Comment