Sama da shekaru biyar kenan wani magidanci Bakatsine da aka bayyana sunansa a matsayin Babangida Dan Kyadi ya gudu ya bar matan sa saboda sun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2015.
Haka kuma Malam Babangida ya yi hijira daga Nijeriya tun daga lokacin da Buhari ya zama shugaban kasa.
Mutumin dan asalin garin Gafai ne dake jihar Katsina.
A tattaunawar sa da majiyar mu ta Katsina Post ta waya, Malam Babangida bayyana cewa a matsayin sa na dan a mutun jam’iyyar PDP, ya yi adawa da yakin neman zaben Buhari a 2015, inda ya dinga kira da kada a zabi Buhari.
“Na fadawa matana cewa su zabi jam’iyyar PDP amma suka bijire min suka zabi APC har suka daga kuri’ar ta su suka nunawa duniya cewa APC suka zaba, har jama’a suka dinga yi min ihu”.
“Abin ya yi matukar bakanta min. Kuma bayan an sanar da cewa Buhari ya ci zabe, sai na kira su na fada musu cewa zan yi musu kaura har sai Buhari ya kare wa’adinsa”, cewar Malam Babangida.
Malam Babangida ya kuma kara da cewa tun daga lokacin da Buhari ya hau mulki bai sake kwana a Nijeriya ba, kuma ya sha alwashin ba zai dawo kasar ba har sai wa’adin Buharin ya kare.
© hutudole
Post a Comment