A rikicin da aka kwasa tsakanin mambobin kungiyar ta’addar Boko Haram da dakarun kasar Nijer a kudu masu gabashin kasar an kashe ‘yan ta’adda 50.

 

Dangane ga bayanan da suka fito daga ma’aikatar lafiyar kasar mambobin Boko Haran sun kai hari da miyagun makamai a wani sansanin soja dake garin Tommour a yankin Diffa.

 

Sojojin Nijer sun kalubalanci harin inda suka kuma yi nasarar kashe mambobin kungiyar Boko Haram 50. Dakarun Nijer sun kuma yi alkawarin fara kaiwa kungiyar ta’addancin farmaki a yankunan Taburu.

 

Sanarwar ta kara da cewa an kama ‘yan ta’adda biyu da kuma karbe makamansu masu dinbin yawa.

 

A makon jiya mambobin Boko Haram sun kai hari a cikin motoci 20 a sansanin sojojin Chetima Wongou inda suka kashe sojoji 8 wasu uku kuma suka bata.

 

Shekaru biyar kenen yankin Diffa na cikin dokar ta baci sanadiyar hare-haren da kungiyar Boko Haram ta fara kaiwa tun daga watan Febrarirun 2015 kawo yanzu.



© hutudole

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top