Tsohon Sanata ya bayyana haka ne, a shafinsa na Twitter inda ya ce maganin cutar corona virus, ba wai sa abun rufe hanci ko wanke hannu ba ne, hanya guda daya ita ce mutane su koma ga Allah.

 

Bayan ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter Dino Melaye, ya kawo wata aya a cikin littafin Bibble ya sanya hoton ayar acikin shafin sa.

 

Ga abinda ayar ke cewa kamar haka:

 

“Lokacin da na kulle sararin samaniya don kada ruwan sama ya sauka, ko kuma na aikowa da al’umma cuta.

 

“Idan har mutane da suke bauta mini za su dawo gare ni su yi addu’a sannan kuma su nemi gafarata akan abubuwan da suka yi, na ba daidai ba, ni kuma zan gafarta musu na yafe musu na kuma cire musu wannan bala’i da na aiko musu.

 

“Yanzu idanuna a bude suke, kuma kunnuwana suna jin duk addu’o’inku,” a rubutun da tsohon sanatan ya wallafa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top