Babban bankin kasa ya ware kusan Naira billiyan 22 don dawo da komadar masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood da Kannywood tare da mawaka.

Bankin ya ware wadannan kudade a matsayin bashi daza a na baiwa masana’antun domin tallafa musu.

Daraktan Sadarwa, Mista Isaac Okorafor, shine ya yi jawabi a yayin taron tattaunawa na hadin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki a kan manufofin shekaru biyar na Babban Bankin Nijeriya (CBN) a karshen mako a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Ya ce, “Babban Bankin na CBN ya kuma sha al’washin tayar da masana’antar da ta kare. “A halin yanzu, Nollywood da Kannywood da masana’antar kade-kaden Nijeriya su ne manyan masana’antar nishadi a Afirka. Ba za mu bar masana’antar ta fadi ba. A shirye mu ke mu tallafawa masu shirya fina-finai a masana’antar.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top