A ranar Laraba ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana samun karin mutane 5 dake dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 wanda hakan ya kawo yawan wanda ke dauke da cutar mutum 8 kenan da aka Samu a Najeriya.
Cikin wanda aka samu dauke da cutar akwai wata mata da jaririnta dan kimanin watanni 6 da haihuwa.
Ba’amurken da ya shigo Najeriya ya mutu a jihar Ekiti kuma ana zargin ya gogawa Direban daya daukeshi daga Legas zuwa Ibadan cutar duk da cewa ba’a samu wata data mai rakiya da cutarba.
Gwamnatin tarayya, Jihar Oyo,Legas da Ekiti sun dukufa neman mutane 800 da ake zargin sun yi ma’amala da mutumin da ya mutu. Ciki hadda wanda suka hau jirgi daya dashi.
An samu Coronavirus/COVID-19 a karin farko a Arewa inda ta bulla a jihar Katsina.
Jihohin Arewa maso yamma zasu kulle makarantu na tsawon kwanaki 30 dan kare yaduwar cutar.
Ta hana taruwar mutane fiye da 50,jihar Ogun ma haka.
Jihar Kwara ta rufe Makarantu.
Gwamnatin tarayya ta hana kasashe 13 shigowa saboda cutar, kasashen su hada da, China, Switzerland, Norway, Netherlands, Faransa, Koriya ta Kudu, Italy, Amurka, Japan, Iran, Jamus, Sifaniya, da Ingila.
Gwamnatin tarayya ta dakatar da baiwa ‘yan kasashen waje bizar nan take.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta dakatar da gasar Premier League har sai abinda hali yayi.
Majalisar tarayya na son shugaba Buhari yawa ‘yan Najeriya jawabi kan halin da ake ciki kan cutar.
Majalisar wakilai na son a daina sallar jam’i,kulle masallatai da coci-coci a fadin Najeriya.
Kasar Amurka ta dakatar da baiwa ‘yan Najeriya bisa.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment