Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajan ta ma iyalan wa’inda suka rasa yan uwan su, da duk wa’inda fashewar Bututun Mai tashafa a yankin Abule Ado karamar hukumar Amuwo Odofin na jihar Lagos a ranan Lahadin nan.
Shugaban kasa ya mika sakon ta’aziyya ga Gwamnatin jihar Lagos da kuma mazauna yankin da Al’amarin fashewar ta shafa, Wanda yayi sanadiyar Raunata wasu da dama da lalata Dukiya masu yawa.
Shugaba Buhari yace;
“Na samu Labarin faruwar wannan abin takaici dayayi sanadin Rayuka da Dukiya.
“Aukuwan irin wannan abin kaico a ko ina bala’i ne ga kasar, haka kuma Kamfanin Mai na NNPC yayi kokarin tantance makasudin Aukuwar lamarin, Na aike da sakon Jajantawa matuka ga wa’inda fashewar ta rutsa dasu, Iyalansu, Gwamnati dakuma Al’umman jihar Lagos.
Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Bangaren Rediyo da Talabijin.
Garba Shehu
Senior Special Assistant to the President
(Media and Publicity)
March 15, 2020
© hutudole
Post a Comment