Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa sabbin ministoci kuru-kuru cewa duk wani mai son ganin sa, sai ya yi kamun kafa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari tukunna.

Buhari ya furta haka a lokacin da ya ke jawabin rufe taron kwanaki biyu na sanin-makakar-aikin da aka shirya wa sabbin ministoci 43, a Abuja.

“ Domin tsarin ayyuka su rika tafiya daidai, ina so duk wani mai son jan hankali na a kan wani batu ko neman ganawa ido-da-ido da ni, to ya nemi izni daga wajen Abba Kyari. Yayin da duk wasu batutuwan da suka shafi bangaren Majalisar Zartaswa ta Ministoci, to tuntubi Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Idan ba a manta ba dai an sha sukar Abba Kyari a matsayin sa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa. Wasu da dama na ganin cewa ya na da karfi sosai a gwamnatin Buhari.

Sai da ta kai ma har uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta yi korafin cewa Kyari ya na wuce makadi da rawa, ko kuma wuce gona da iri.

Masu gani da kuma tunanin cewa Abba Kyari kamar ya zama kadangaren-baki-tulu a gwamnatin Buhari a zango na farko daga 2015 zuwa 2019, sun cika da mamaki ganin ya sake maida shi a matsayin sa, bayan ya yi nasarar a zaben shugaban kasa na 2019.

Buhari ya tunatar da sabbin ministocin cewa mafi yawan ‘yan Najeriya duk talakawa ne masu tunanin wurin kwanciya da kuma yadda za su samu abincin yau da na gobe.

“ Babban nauyin da ke kan mu a matsayin mu na shugabanni shi ne mu ga mun samar wa wadannan dimbin talakawa abubuwan da suka bukata a rayuwa na tilas.”

Daga nan kuma sai Buhari ya koma ya na nanata matsalolin da gwamnatin sa ta gada daga gwamnatin Goodluck Jonathan da ya gada.

“ Aikin gwamnati dai abu ne mai walahar gaske. Sau da dama ma za ka yi ka gama ba a gode maka ba. Ina jan hankalin ku da ku tabbatar kun yi aiki cikin gaskiya da rikon amana tare da bin ka’ida.

Ga wadanda a yanzu ne za su fara aikin minista a karo na farko, zan so ku dauki darasi da kwaikwayo daga ministoci da gwamnonin da shuka shude a baya.” Inji Buhari.

Me za Ku ce

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top