Hukumar lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, matasa su yi hankali da cutar Coronavirus/COVID-19 saboda suma zata iya kamasu ta kwantar dasu, watakila ma har ta kaisu ga halaka.

 

WHO ta yi wannan kirane saboda bayanan dake watsuwa tsakanin al’ummar Duniya cewa cutar bata tasiri akan matasa.

 

Cutar dai wadda ta samo asali daga kasar China, Birnin Wuhan ta kashe sama da mutane Dubu 11 zuwa yanzu, sannan kuma ta kama mutane kimanin dubu Dari 250.

 

Yankin Turai ya kwacewa China yawan cutar inda a yanzu kasar Italiya ta zama ta gaba wajan yawan masu cutar da wanda take kashewa. Mutane 627 ne suka mutu a jiya Juma’ akwai wanda hakan ya kai yawan mutanen da suka mutu 4,032 a kasar.

 

Daraktan hukumar ta Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus da yake magana a wani taron manema labarai da aka shirya ta yanar gizo daga hedikwatar hukumar dake Geneva yace matasa su daina ganin cutar ba zata musu ila ba.

 

Yace koda ba dan kansu ba ya kamata su kula da irin halin da sauran mutane zasu shiga ciki su daina cudanya da yawa dan hakan zai karawa cutar muni.

 

Matsakaitan cikin wanda suka rasu a kasat Italiya dai na da shekaru 78 ne yayin da kaso 1 cikin 100 ne kawai namasu shekaru kasa da 50 suka mutu dalilin cutar.

 

Cutar ta fi kamari akan wanda suka manyanta daga shekaru 80 zuwa sama



© hutudole

Post a Comment

 
Top