Ministan kiwon Lafiyar Nijeriya, Osagie Ehanire ya bayyana cewa jaririya ‘yar sati shida na cikin karin mutane biyar da suka kamu da cutar coronavirus a Nijeriya.

Ehanire ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Laraba inda ya ce wannan jaririya na daga cikin wadanda aka samu suna dauke da cutar a kasar nan ranar Laraba.

Ya kara da cewa daya daga cikin wadanda suka shigo Nijeriya da cutar ya shigo ne ta iyakar Nijeriya da wasu kasashe ta kasa.

Sannan duk sauran wadanda suka kamu suna da tarihin zuwa kasashen Amurka da Uk.

A ranar Laraba ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa wasu mutane biyar sun kamu da cutar coronavirus a kasar nan.

Bincike ya nuna cewa mutane biyar din da suka kamu da cutar sun yi tafiya zuwa kasashe Amurka da UK.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top