Da yammacin jiya ne, a ofishin hukumar Hisbah na Jihar Kano Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Muhd Sani Ibn Sina ya sami zarafin ganawa da Sharu Aminu Sharif Shu’aibu da ke unguwar Kofar Wambai a birnin Kano.

 

Indan mai sauraro zai iya tunawa, sharu Aminu Sharif Shu’aibu, shine mahaifi ga Yahaya Sharif Aminu Baban Gona, mawakin da ya yi batanci ga Manzon Allah ta cikin wani faifan bidiyo wanda aka watsa a yanar gizo, wanda hakan ya tashi hankalin daruruwan musulmi, inda matasa suka shirya zanga-zangar nuna bacin rai izuwa ga hukumar Hisbah da ke unguwar Sharada.

 

Inda Babban kwamandan hukumar Hisbah ya karbi wadanda suka shirya zanga-zangar tare da alkawarin bibiyar wannan al’amari har sai an kai ga nasara.

 

Bisa hakan Dr. Harun Ibn Sina ya sami nasarar ganawa da Uban wan nan yaro wanda ya yi batanci kamar haka. Cue in insect.(1) Sharu Aminu Sharif Shu’aibu.

 

Da ya ke mai da jawabi, Dr. Harun Ibn Sina ya ce hukumar Hisbah za ta cigaba da bibiya har sai ta sami zarafin cafko wannan mai katobara ga ma’aikin Allah tare da daukan matakin da ya dace da shi. Cue in insect (2) kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Ibn Sina.

 

Lawan Ibrahim Fagge
Public Relation Officer.



© hutudole

Post a Comment

 
Top