Kasar Japan ta bayyana cewar su ta bangarensu babu abin dazai hanasu gudanar da gasar guje-guje da tsalle-tsalle daza ayi a babban birnin kasar ta Japan wato Tokyo.

Wannan magana ta fitone daga bakin Prime Minister na kasar inda yace gasar ta Olympic tana nan babu gudu babu ja da baya sudai sun shirya tsaf dangane da batun.

Wasu kasashe da wasu masanan suna ta ganin cewa tunda wasane na cudanya da ma’amala tsakanin kasashen duniya to kawai ya kamata a sake sanya ranar yin wannan gasa ta Olympic a nan gaba tunda har yanzu cutar tanaci gaba da yaduwa ka’in da na’in.

Itama kasar Japan tuni dubban mutane suka kamu da wannan cuta inda a sanadin cutar sama da mutane 400 ne suka rasa ransu acan kasar ta Japan.

Tuni dai aka dakatar da gasannin yankin turai a sakamakon kara yawaitar masu dauke da cutar corona wanda aka fi sani da covid 19, wanda ko a jiya ma mun rawaito muku cewa gasar Euro 2020 an dakatar da ita harzuwa wani lokaci, haka zalika a kasa Najeriya shugaban kasa ya dakatar da bikin wasanni na Edo, duk a sakamakon fargabar bullar wannan cuta ta Corona.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top