Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta sanar da bude wasu katafarun dakunan gwajin kwayar cutar coronavirus a jihohi uku na kasar da birnin tarayya Abuja.

Dakunan gwajin dai an bude su ne a jihohin hudu Legas, Edo, Osun da kuma birnin tarayya Abuja

Hukumar NCDC din ta bayyana hakan a shafinta na twitter a jiya Laraba.

Sa’annan NCDC din ta kuma kara da cewa duk wanda za a yi wa gwajin na COVID19 za a yi masa ne kyauta batare da ko kwaban sa ba.

Zuwa yanzu dai an samu bullar cutar a jikin mutum biyar a Nijeriya inda hakan ya yi sanadiyyar dakatar da tarukan jama’a a wasu sassan kasar.

Wanda biyo bayan hakan wasu jahohin sun ayyana rufe makarantu domin Kara dakile yaduwar cutar.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top