Yayin da masana kimiya ke gudanar da bincike domin samun kyakkawar fahimtar cutar Coronavirus kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga mutane musamman masu shan taba ko masu shakar hayakin taba da su nisanta kansu da haka cewa busa taba da shakar hayakin ta na sa a gaggauta kamuwa da cutar.
WHO ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da masana kimiya suka gudanar a wuraren gwaji 55,2924 dake kasar Chana.
Sakamakon binciken ya nuna cewa dayawa daga cikin mutanen da corononavirus ta yi mummunar ko suka mutu na dauke da wasu cututtuka a jikinsu da suka hada da cututtukan dake kama zuciya, nunfashi, hawan jini, ciwon siga, daji, tarin fuka da makamantan su.
Sakamakon ya kuma kara nun cewa mutanen da suka kamu da irin wadannan cututtuka sun kamu da su ne a dalilin shan taba da suka yi a shekarun baya ko suke yi har yanzu.
Kungiyar kiwon lafiyar ta ce duk da cewa babu tabataccen sakamakon binciken da ya nuna cewa akwai alaka da shan taba da cutar Coronavirus amma kamata ya yi mutane su kiyaye domin guje wa kamuwa da cutar.
© hutudole
Post a Comment