Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya ce gwamnatinsa ta hango matsalolin tattalin arzikin da za su iya auka wa kasar saboda bullar annobar coronavirus, da ta mamaye duniya.

 

Sai dai ya ce za su yi amfani da duk hanyoyin da suka dace wajen kare al’ummominsu.

 

Muhammadu Buhari na bayyana haka yayin ganawa da kwamitin kwararrun masu ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki karkashin jagorancin Farfesa Doyin Salami ranar Talata.

 

Ya ce abubuwa da dama sun taka rawa ga faduwar farashin man fetur a duniya wanda ke tsalle a tsakanin dala 29 zuwa dala 30 cikin ‘yan kwanakin nan, sabanin mizanin dala 57 kan ganga guda da Najeriya ta yi hasashe a kasafin kudinta na bana.

 

Sanarwar da babban mashawarcin shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar ta ambato Shugaba Buhari na cewa kare mutane daga halin bazata na tattalin arzikin duniya da abubuwan da suka shafi faduwar farashin man fetur su gwamnatinsa za ta bai wa fifiko a wannan lokaci.

 

Sanarwar ta kuma ambato shugaban kwamitin kwararrun kan tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami na fayyace wani irin yanayi da ka iya auka wa tattalin arzikin Nijeriya, matukar annobar COVID-19 ta dauki tsawon lokaci.

 

Ya ce bunkasar tattalin arzikin kasar na iya fuskantar tafiyar hawainiya, don kuwa fannin bukatu da safarar kaya na tattalin arzikin duniya zai tabu.

 

Haka kuma ana iya shiga halin rashin tabbas, wanda zai rage kwarin gwiwar da mutane ke da shi, yayin da gwamnatoci za su rika yin gaban kansu maimakon ayyukan hadin gwiwa.

 

Haka kuma tasirin cutar na iya janyo karin faduwar farashin man fetur da sanya wa a kara killace mutane ba shiga ba fita a fadin duniya.

 

Za kuma a fuskanci kwantan man fetur saboda zai cika kasuwa, ga rashin daidaiton kasuwanci da kuma faduwar ajiyar kudaden ketare baya ga karuwar rashin aikin yi.

 

Kwamitin ya nunar cewa kasashe da dama a fadin duniya na iya shiga koma-bayan tattalin arziki, don haka ya bukaci yin aiki tukuru ta yadda Najeriya za ta iya kubuta.

 

Haka zalika kwamitin ya ba da shawarwarin da suka hadar da yiwuwar bitar kasafin kudin bana, ta yadda zai ba da karfi ga fannin kula da lafiya.

 

Da mayar da karfi kan ayyukan da gwamnati ta kusa kammalawa da kuma wanda ke da tasiri ga rayuwar jama’a da zabge kason da ta ware wa ayyukan yau da kullum.

 

Haka zalika kwamitin ya bukaci gayyato bangaren ‘yan kasuwa don karfafa kayayyakin aiki a bangaren lafiya da bunkasa kudaden shigar gwamnati.

BBChausa.



© hutudole

Post a Comment

 
Top