Gidauniyar Attajirin Chinan nan, Jack Ma za ta taimaka wa daukacin kasashen Afrika 54 da kayayyakin yaki da cutar Coronavirus, inda za ta bai wa kowacce kasa a nahiyar kyallayen rufe hanci dubu 100 da akwatinan kayayyakin gwaje-gwaje dubu 20, da kuma rigunan kare kai daga cutar dubu 1.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Jack Ma da ya assasa rukunin gidauniyar Alibaba, ya jadadda muhimmancin hubbasawa a daidai lokacin da cutar Coronavirus ke ci gaba da karade sassan duniya tare da lakume rayuka.
Za a isar da wadanann kayayyakin jinya zuwa birnin Addis Ababa na Habasha, bayan Firaministan kasar, Abiy Ahmed ya amince ya jagoranci sanya ido wajen rarraba wadannan kayayyaki a sassan Afrika.
Jack Ma ya ce, ba za su iya kauda kai daga barazanar da Afrika ke fuskanta ba tare da tunanin cewa, wannan nahiya mai yawan al’umma biliyan 1.3, za ta iya kare kanta da annubar Coronavirus.
Attajirin ya kara da cewa, a yanzu ne za a dauki riga-kafi tare da zama cikin shirin tunkarar annubar, yana mai cewa, Afrika za ta iya amfana daga darasin da sauran kasashen duniya suka dauka daga wannan cuta.
Baya ga kasashen na Afrika, har ila yau gidauniyar Jack Ma, ta taimaka wa wasu kasashen duniya da kayayyakin yaki da Coronavirus da suka hada da Japan da Koriya ta Kudu da Amurka da Italiya da Spain da kuma Belgium.
© hutudole
Post a Comment