An kama wadanda ake tuhuma da kashe wasu ‘yan mata uku wadanda dukkansu dalibai ne a Kwalejin Ilimi ta Minna, a daidai lokacin da suke kokarin sayar da sassan jikin ‘yan matan da suka kashe. kamar yadda jaridar leadership ta rawito.

Wadanda ake tuhumar masu suna, Musa Smart, Ndakolo James da wani boka mai suna, Bature Nathaniel, ‘yansanda sun kama su ne a sassa daban-daban na Jihar Neja.

A lokacin da ‘yansandan suka yi holin wadanda ake tuhumar a hedikwatarsu, sun ce sun sace ne tare da kashe ‘yan matan, sannan suka nemi sayar da sassan jikinsu ga wani mai suna Musa Smart, wanda suka yi zargin ya alkawarta masu biyansu naira milyan Biyar a kan sassan jikin na su.

Tun a farkon shekarar nan ce aka shelanta bacewar wasu ‘yan mata biyu, Oladepo Blessing, da Oluwasemilore Mary, wadanda dalibai ne a Kwalejin ilimin ta garin Minna,

Daya daga cikin mutane ukun da ake tuhuma mai suna, Musa Ndakolo, ya ce an yi masu alkawarin biyansu naira milyan Biyar ne domin su samo nonon hagu da hannayen ‘yan mata. Ya ce sai bokan ya ki biyansu abin da ya yi masu alkawarin duk da cewa sun biya masa bukatar na shi.

Wani kuma cikin wadanda ake tuhumar mai suna Musa Smart cewa ya yi, sun dauki daliban ne da misalin karfe 9:30 na dare a lokacin da suke dawowa daga makaranta za su koma gidajen kwanansu a bayan da suka kammala karatunsu na dare.

Rundunar ‘yan sandan Jihar, Wasiu Abiodun ya ce, ya tabbatar da faruwar lamarin.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top