A yayin da ake ci gaba da fama da annobar cutar Coronavirus/COVID-19 data addabi Duniya Najeriya ma ta dukufa dan ganin ta magance yaduwar cutar.

 

Gwamnan Jihar Legas Sanwo Olu ya bayyana cewa mutane 11 ne a jihar aka samu da cutar. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

 

Mutumin farko dan kasar Italiya da aka fara samu da cutar a Najeriya ya warke inda Rahotanni suka bayyana cewa an sallameshi daga Asibiti.

 

Gwamnatin tarayya ta kulle duk filayen sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake fadin Najeriya in banda na Abuja da Legas. Suma wasu Rahotanni na bayyana cewa nan gaba kadan za’a iya kulle su. Amma gwamnati tace ba zata hana zirga-zirga a cikin kasar ba.

 

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da kayan abinci da Magunguna, NAFDAC  ta bayyana cewa ta bayar da damar amfani da Chloroquine wajan magani a Najeriya. Saidai tace bawai za’a ayi amfani da Chloroquine wajan maganin  cutar Coronavirus/COVID-19 bane. Hakan na zuwa lokaci kadan bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa za’a iya amfani da Chloroquine din wajan maganin cutar Coronavirus amma daga baya hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar ta musanta wannan batu.

 

A jihohin Nasarawa da Ekiti an kilace mutane 47 saboda Coronavirus/COVID-19.

 

A jihar Ekiti an kilace mutane 42 da suka yi alaka ta kai tsaye da wadda ba ta kai tsaye ba da mutuminnan dan kasar waje da ya mutu a jihar wanda ake tsammanin yana dauke da cutar.

 

Gwamnatin jihar tace mutanen da aka killace basu fara nuna wata alama ta cutar ba amma nan da kwanaki 14 za’a musu gwaji dan tabbatar da irin halin da suke  ciki.

 

A jihar Nasarawa ma mutane 5 ne aka killace ‘yan gida daya da suka fito daga jihar Ogun wanda kuma suka fara nuna alamar cutar ta Coronavirus/COVID-19.

 

Jihohin Legas da Oyo da Eikiti sun dakatar da taron jama’a da yawa sun kuma kulle duk wasu guraren dake tara jama’a da yawa. A jihar Ekiti kam gwamnatin jihar ma cewa ta yi ma’aikata su zauna a gida su rika aiki daga gida.

 

A jihar Kaduna kuwa gwamnatin ta hana taron ibada, Sallar Jam’i data Juma’a da tarukan da suka wuce na mutane 10. Hakanan an hana ayyukan ibadar Kiristoci da rufe makarantu na tsawon kwanaki 30. Duk da ba’a samu wani dauke da cutar ba a jihar amma gwamnatin jihar ta ce tana daukar matakan rigakafi.

 

Hukumar jarabawar kammala Sakandare ta WAEC ta dakatar da jarabawar saboda Coronavirus/COVID-19.

 

Saidai ita kuma hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB da ake kan rubuta jarabawar a yanzu, tace ba zata dakatar da rubuta jarabawarba saboda Coronavirus/COVID-19.



© hutudole

Post a Comment

 
Top