Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da gudummawar naira milyan goma sha biyar ga Kungiyar Izala ta kasa a birnin tarayya Abuja.
Gwamnan ya samu wakilcin Marafan Waziri Hon Abdullahi Maigwandu kana Kwamishinan Ma’aikatar lamurran Addini ta jahar Sokoto.
Taron wanda aka yi filin Old Parade Ground dake Area 10 a Abuja, an yi shine kamar yadda aka saba yin sa a duk shekara.
Kungiyar Izala ta kasa, ta bakin Shugaban ta, ta godewa Gwamna Tambuwal akan kokarin da yake yi wajen taimakawa addinin Islama.
Ya kara da cewa, maigirma Gwamna Tambuwal bai taba kasawa ba wajen bayar da gudummawa a duk lokacin da ake neme shi da ya bayar, da wasu da yake yi a kashin kansa.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya saka masa da mafificin alkairinsa ya biya masa dukkanin bukafun sa na alkairi duniya da lahira.
© hutudole
Post a Comment