Tun bayan bullar jita jitar da ke yawo a kafafan sadarwa cewar Sunusi Lamido shi ne yafi can-cantar maye gurbin Shugaban Kasa Buhari a shekarar 2023.
Martani ke ta bayyana daga bakunan yan’ Siyasa, shima dai tshohon Sanatan Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijai Shehu Sani ya shawarci Tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido da kada ya kuskura ya shiga harkar Siyasa ko yin takarar kujerar Shugaban Kasa a shekarar 2023 mai zuwa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce, “Ka huta lafiya cikin kwanciyar hankalin tare da iyalanka ba tare da wata wahala ba.
Sanatan ya kara da cewa Ka guji mutane daban-daban da kungiyoyi masu kokarin jawo ka cikin siyasa kuma ka guji masu son amfani da kai a matsayin tsanin da zasu taka dan su cimma wata manufar tasu.
A cewar sa Sunusi Lamido ya isa gwarzo ya kuma bayyana masu neman jawo shi harkar siyasa da su nemi wani shahidin a wani wurin.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment