Ministan Shari’a Abubakar Malami ya nisanta kansa akan batun tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da kora shi garin Awe da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi.
Malami ya ce babu ruwan sa sannan bashi da masaniya akan abubuwan da suka faru a Kano.
Malami bai san abinda aka yi a Kano ba game da tsige sarki Sanusi II da kora shi da aka yi garin Awe. kuma ba zai ce komai a kai ba tunda maganan na kotu.” Inji kakakin ofishin ministan.
Idan ba a manta ba Kotu a Abuja ta umarci mahukunta a Najeriya da su kyale tsohon sarkin Kano Sanusi ya wataya yadda yake so a ko ina a fadin kasar nan ban da jihar Kano.
Bayan saurarar karar yanzu an dage zaman kotun har zuwa 26 ga watan Maris.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment