Wani Matashi me suna Shafi’u Haruna dan kimanin shekaru 27 ya kashe budurwarsa bayan da aka zargeshi da dirka mata cikin shege.

 

Shafi’u Haruna ya ja budurwarsa, Hamsiya Lawal ‘yar kimanin shekaru 14 bayan garinsu, Dorawar Natiba dake garin Birdigau karamar hukumar Kankara inda ake zarginshi da amfani da wani murgujejen Dutse wajan fasa mata kai kuma ta mutu, kamar yanda kakakin ‘yansandan jihar,SP Gambo Isah ya shedarwa manema labarai.

 

Haruna ya aikata laifinne a watan Disambar Shekarar 2019 data gabata amma ba’a samu kamashi ba sai ranar talatar makon daya gabata.

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top