ALHAKINA NE DANA SAURAN MUTANE YA FARA BIBIYAR DATTI ASSALAFIY; Inji Munirat
Matashiya Munirat Abdulsalam ta chachchaki masu sukar bayyana Hotunan Datti Assalafy, don an bayyana Hotunan sa.
Munirat Ta Bayyana Cewa Lokacin Da Datti Assalafiy Ya Sanya Wasu Mutane Suka Ringa Bibiya ta Suna Neman Rayuwata Wallahi Nasha Wahala Har Aman Jini Sai Da Nayi A Kokarin Cetar Rayuwata Daga Hannunsu
Na yarda cewa abinda Nakeyi Ba Dai Dai Bane Ya Sabawa Allah, Kuma Harga Allah Inada Niyyar Tuba, Amma Kwatsam Sai Naga Wani Mutum Mai Suna Datti Yana Bada Sanarwa A Shafin fesbok Wai a Kulle Shafina na Fesbuk Kuma a hallaka ni wai Ina bata tarbiyyar mutane.
Dole Inaji Ina gani nabar mahaifata naje na boye Kaina Saboda Kullum Mutanen Datti kokarin halakani Sukeyi Suna tunanin hakan jahadi ne.
Na dade Ina tunanin Cewa Wane Irin Addini Ne Datti Yakeyi Wanda Babu Tausayi Koh Jinkai Acikinsa
Maimakon suyi mini nasiha tunda Suna ganin abinda nake aikatawa Ba dai dai bane amma Sai Suke neman halakani.
Ranar Dana Koma Karbar Kalmar Shahada Na Tambayi Malamin Da Naje Wajensa Cewa Shin Dama idan mutum yana aikata Irin Laifina Hukuncin Kisa Akansa Ku Kuma Nasiha Za ayi masa, Malam Yayi Min Nasiha Tare Da Cewa Abinda Datti Ya Aikata Ba Dai Dai Bane
Ta dora Alkurani a Kai, Munirat tace Wlh Wlh Wlh nayi rantsuwa da Alquranin dake hannuna Sau Uku Datti yana turo mutane su halakani saboda kawai inayin abinda yake ganin sabon Allah ne
Na dade ina tunanin cewa mutukar irinsu datti ne masu daraja acikin muslinci Tom na rantse da Allah babu abinda sukeyi sae cutar da addinin
Bayan na sake muslinta kullum idan nayi sallah sai nayi addua cewa Abinda Datti Assalafiy yayi min Allah yai mini sakayya cikin gaggawa kuma ahamdulillahi gashi tunba aje ko ina ba Allah Ya Fara sakamin kamar yadda yayi alkawarin cewa yana karbar adduar wanda aka zalunta.
Sources: Jaridar DimokuraÉ—iyyar
©HausaLoaded
Post a Comment