Masu karatu, ina muku kyakkyawar gaisuwa assalamu alaikum warahmtullah. Barkan mu da sake haduwa a wannan makon a cikin wannan fili naku mai tarin farin jini. Ina fata uwargida, amarya da sauran abokan zama kowa yana nan cikin koshin lafiya.

A wannan makon, za mu tattauna ne a kan wani abu mai muhimmanci ga zamantakewar aure a tsakanin maigida da uwargida ko kuma in ce a tsakanin maigida da matansa. Wannan muhimmin abu kuwa shi ne koi ta ce ‘Godiya’. Abin da ake nufi da godiya shi ne, idan wani ya yi maka wani abu da ya dadada maka rai ko kuma ya ba ka wani abu domin girmamawa a gare ka, sai ka nuna jindadinka a zuciya, abin ya bayyana a fuska, sannan a furta kalmar “na gode” da baki. Wannan zai sa wanda ya yi abin ya ji dadi kuma ya san cewa kai da aka yi wa ba Butulu ba ne. Uwargida, amarya mu tabbatar da cewa mun dabi’antu da wannan a ko wane lokaci.

Domin rashin godiya ga duk abin da maigida zai yi ko ya kawo na daga cikin abubuwan da ke haifar da matsaloli a gidajen aure.Wata mace duk abin da maigida zai shigo da shi ko ya mata kyautarsa to ba godiya ko yabawa ,hakan kan tundura mazaje har ya jawo rigima matuka.

Kuma hakan kan rage kima da darajar mace wurin mijinta.

A duk lokacin da maigida zai kawo wani abu to yana da kyau mace ta yaba ta Kuma yi godiya.Musamman wannan zamani da komai yake da wahalar samuwa.Wasu mata kan hangi abin da mijin wata makociya ko kawa ke ma ta,sai su sa wa zuciyarsu lallai su ma sai irinsa.Wannan abin ya taka muhimmiyar rawa matuka wurin jawo matsalolin ma’aurata har ma da mace _macen aure.

Duk wata mace tagari yana da kyau ta yaba da kokarin mijinta akan duk wata hidima da yake mata ,hakan zai daukaka darajarta a idonsa ,ya Kuma sama Mata nitsuwa da kwanciyar hankali a gidan aurenta.Haka nan unangiji zai rufa Mata asiri ya Kuma buda Mata hanyoyin alheri .Bashi daga cikin tarbiyya mace ta nunawa miji Bata m gode ba akan abin da ya ke Mata.

Shawara…

Shawarata ga ‘yan uwa mata anan ita ce ,a kullum kar mu kalli gidan wata,ko mijin wata balle mu sa rai akan abin da ke faruwa a wannan gida.Allah da ya hallice mu ya banbanta mu ta hanyoyi masu yawa saboda haka kada walwalar gidan wata ya dakushe mana farin ciki a gidajen aurenmu.Duk abin da maigida ya kawo ko yakeyi mu karba da farin ciki Kuma muyi godiya ,hakan zai sama mana nitsuwa cikin zukatanmu .

Allah yasa mu gyara.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top