ABUBUWAN DAKE BATA AZUMI DA WANDA YA HALATTA GA ME AZUMI A SUNNAR ANNABI(S.A.W).
**************************************************
Darasi Na uku(3)na Qarshe cikin # AZUMI .
ﻓﻘﻪ ﺍﻟﺴﻨﻪ (fiqhus sunna).
#Azumi shine kamewa Daga Barin ciki da sha Da jima'i tundaga Bullowar Alfijir Har izuwa Faduwar Rana Da niyyar yin Ibada ga Allah(S.W.T).
ME KE BATA AZUMI ?
Abu na farko shine:-
1-RIDDA, wato fita daga Musulunci.
Koda ta hanyar furta wata kalmace mummuna.
2--CI ko SHA ,da gangan ba tare da uzuri ba,misali kamar na mantuwa.
3-HAILA ko NIFASI, sai dai a kirga kwanakin da aka sha a rama su bayan Ramadan.
4-JIMA'I, Tarawa da mutum ko dabba ko ma da menene.
5-Fitar maniyyi dan sha'awa ko da jima'i ko babu.
6-Kakaro amai da gangan.
7-Hauka,wato gushewar hankali.
Dade sauransu.
Idan namiji da mace suka sadu da rana a cikin watan Azumi to, azuminsu ya baci, sai su rama kuma su yi kaffara.
Don fadin sahabin Annabi (saw)Abu Huraira (R.A) ya ce, wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune sai wani mutum ya zo ya ce, ya Rasulullahi, na halaka, sai Annabi ya ce da shi, mai ya halaka ka? Sai ya ce, na sadu da matata a cikin watan Azumi da rana, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, za ka sami abin da za ka ’yanta bawa? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, za ka iya yin Azumi watanni biyu a jere? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, shin za ka sami abin da za ka ciyar da miskinai sittin? Sai ya ce, a’a, sai mutumin ya zauna a wajen Annabi har aka kawo wa Annabi buhun dabino. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, dauki ka yi sadaka da shi, sai ya ce, ai duk cikin Madina babu wanda ya fi ne bukata. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi dariya har sai da hakoransa suka bayyana. Sannan ya ce, dauki ka je ka ciyar da iyalanka.
8-shigar abu maqoshi,misali gari ko wani Abu mai kamar kura ,amma anyi Rangwame ga Wanda su sana'ar sune dole sai kura ta tashi ,zasuyi iya iyawarsu don karta shige maqoshinsu Sauran abinda yafi qarfinsu sai subarwa Allah.
Wallahu a'alam.
ME KE HALATTA GA MAI AZUMI ?
Allahu (S.W.T) ya yi wa Musulmi sauki lokacin Azumi da daddare su sadu da iyalansu.
ﻗَﺎﻝَ ﺗَﻌَﺎﻟَﻰ : " ﺃُﺣِﻞَّ ﻟَﻜُﻢْ ﻟَﻴْﻠَﺔَ ﺍﻟﺼِّﻴَﺎﻡِ ﺍﻟﺮَّﻓَﺚُ ﺇِﻟَﻰ ﻧَﺴَﺎﺋِﻜُﻢْ ". ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 187 ﺁﻳﺔ )
Ma'ana: Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: An halasta gare ku a daren Azumi ku kusanci matanku.
(Suratul Bakara: aya ta 187/ ١٨٧ ).
An karbo daga Barra’u ya ce, yayin da Allah (S.W.T) ya wajabta Azumin Ramadan, sahabbai sun kasance ba sa saduwa da iyalansu da daddare, har sai da Allah ya saukar da wannan ayar.
Babu laifi mai Azumi ya wayi gari da janaba a cikin watan Ramadan.
ﻋَﻦْ ﻋَﺎﺋِﺸَﺔَ ﻭَﺃُﻡُّ ﺳَﻠَﻤَﺔ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻨْﻬُﻤَﺎ : " ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻛَﺎﻥَ ﻳُﺪْﺭِﻛُﻪُ ﺍﻟْﻔَﺠَﺮَ ﻭَﻫُﻮَ ﺟُﻨُﺐٌ ﻣِﻦْ ﺃَﻫْﻠِﻪِ ﺛُﻢَّ ﻳَﻐْﺘَﺴِﻞُ ﻭَﻳَﺼُﻮﻡُ ". ( ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻯ )
Ma'ana:
An karbo daga Aisha da Ummu-Salama (R.A) suka ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance alfijir yana riskarsa yana mai janabar saduwa da iyalansa, sannan ya yi wanka kuma ya yi Azumi. (Bukhari ne ya rawaito).
Abu Dawud ya rawaito Hadisi daga Nana Aisha (R.A) ya ce, ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana runguma ta lokacin da yake Azumi kuma ni ma ina Azumi. (Abu Dawud).
Idan mutum ya sumbaci matarsa ko ya rungume ta har ya fitar da maziyi to ba komai a gare shi.
Idan kuma mutum ya rungumi matarsa ko ya sumbace ta, lokacin duk suna Azumi har dayansu ya zubar da maniyi to Azumin wanda ya zubar da maniyyin ya baci kuma sai ya rama Azumi.
3. Yin Kaho: Idan mutum yana Azumi sai ya sa aka yi masa kaho, shi ma ba komai a gare shi.
ﻋَﻦِ ﺍﺑْﻦِ ﻋَﺒَّﺎﺱٍ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ﻗَﺎﻝَ : " ﺍﺣْﺘَﺠَﻢَ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲُّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻭَﻫُﻮَ ﺻَﺎﺋِﻢٌ ". ( ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻯ )
An karbo daga dan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya yi kaho a lokacin da yake Azumi.
(Bukhari ne ya rawaito).
4. Sa Kwalli: Anas dan Malik (R.A) ya kasance yana sa kwalli lokacin da yake Azumi.
Wallahu a'alam.
HUKUNCIN KIN YIN AZUMIN RAMADAN!
Duk wanda ya ci abinci da rana da gangan a cikin watan Ramadan ba tare da wani uzuri da shari’a ta halatta ba, babu shakka azabar da za a yi masa mai tsanani ce. Kuma ko da zai mutu yana Azumi ba zai zama ya cike wannan ranar da ya ci ba.
ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻰ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠﻪ ﻋَﻨْﻪُ ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ : " ﻣَﻦْ ﺃَﻓْﻄَﺮَ ﻳَﻮْﻣًﺎ ﻓِﻲ ﺭَﻣَﻀَﺎﻥَ ﻓِﻲ ﻏَﻴْﺮِ ﺭُﺧْﺼَﺔ ﺭَﺧَّﺼَﻬَﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﻟَﻪُ، ﻟَﻢْ ﻳَﻘْﺾِ ﻋَﻨْﻪُ ﺻِﻴَﺎﻡَ ﺍﻟﺪَّﻫْﺮِ ﻛُﻠِّﻪِ ﻭَﺇِﻥْ ﺻَﺎﻣِﻪُ ". ( ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻯ )
Ma'ana:
Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
Wanda ya ci abinci a rana daya daga cikin ranakun Ramadan ba tare da wani sauki da Allah ya yi masa ba,misali yana cikin halin lalura to, ku da zai azumci baki dayan zamaninsa bai rama ba.
Rawahu Abu dauda da Ibn maja.
RANAKUN DA AKA HANA AZUMIN NAFILA.
1-Ranakun Idi guda biyu, wato ranar karamar sallah da babbar sallah.
2-Hakanan kwanakin ukun da ke gaban ranar babbar sallah (Ayyamut tashrik) sai da uzuri.
3-Kebantar ranar Juma'a kawai, sai dai ka hada ta gabanta ko ta bayanta.
4-Kebantar ranar Asabar kawai, sai dai ka hada gabanta ko ta bayanta.
5-Hakanan ranar shakku, kamar ana zaton gobe Ramadan zai kama ko kuwa.
6-Hakanan yin Azumi kullum ba hutawa kullum.
7-Hakanan matar da mijinta yake nan a gari sai da izininsa.
8-Hakanan jeranta azumi ba tare da sahur ba ko buda baki, ayi kwanaki da kwanaki ana haka.
Wallahu a'alam.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment