Tsamarin da rashin jituwar da ke tsakanin masana’antar Kannywood da shugaban hukumar tace finafinai, Isma’il Afakallahu, ya sanya masu sana’ar shirin fim din Hausa a jihar Kano juya wa gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje baya.
Lamarin ya fito fili bayan gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar, inda rana-tsaka a ka wayi gari ’yan Kannywood da dama sun daina tafiyar gwamnatin Ganduje, wanda kafin zuwan wannan lokaci su ne kan gaba wajen tallata gwamnatin, inda a ka fara ganin su su na yi ma sa wakokin zambo; lamarin da ya ke daure wa da dama kai har a ke zargin ’yan fim da yin butulci.
To, amma binciken da LEADERSHIP A YAU ta gudanar ta hanyar jin ta bakin yawancin masu sana’ar ya nuna cewa, ba haka siddan su ka juya bayan ba; sun yi haka ne saboda jikakkiyar da ke tsakaninsu da Afakallahu.
Wasu wadanda su ka nemi a sakaya sunansu sun nuna cewa, shugaban hukumar tace finafinan ya babbake komai ya hana su su bayyana wa gwamna hakikanin matsalolin da ke damun su, inda kullum a ke yiwa gwamnan ’yar burun-burun.
Hatta horar da su da a ka yi, har kawo yanzu gwamnati ta kasa ba su takardar shaida ko kuma jari kamar yadda a ka yiwa dukkan masu sana’ao’in da a ka horar a jihar. Haka nan alkawarin da gwamna ya dauka na ba wa kundiyarsu mota, ita ma shiru ka ke ji, wai malam ya ci shirya, wato batunta ya sha ruwa kenan.
Sun kara da cewa, wani abu da ya ke addabar su shi ne, tun lokacin da a ka nada Afaka a matsayin shugaban hukumar ya dawo da salon kama su ya na kai su kotu a na cin tarar su, wasu kuma a na daure su. Sun bayar da misali da yadda Afaka ya sa a ka daure Alhaji Salisu Chali da kuma yadda ya sa addabi Marigayi Rabiu Arrahuz har ta kai ga ya koma yin farauci, inda ya kwantsama hatsarin mota ya rasa ransa, baya ga yadda ya kori Alhaji Sani Rainbow, wanda ya na cikin manyan ’yan kasuwar fim da furodusoshi da dama su ka dogara da shi, wanda hakan rashin irinsu ya sa ’yan fim da dama su ka karye.
Bugu da kari, sun yi korafi kan yadda su ka ce Afaka ya yaudare su kan batun bude ofisoshin kananan hukumomi na hukumar da sunan za a bunkasa mu su sana’a, amma har kawo yanzu babu amo babu labari.
Sannan kuma batun ba su rancen kudi da a ka dade a na yi mu su romon baka, shi ma ya sha ruwa, baya ga azabar gaba da su ka ce shugaban hukumar ya na yi da mafi yawan masu sana’ar da ke da tasiri a kasuwar shirin fim a jihar.
Bayanai sun nuna cewa, fitaccen Jarumi Ali Nuhu ya yi iyaka bakin kokarinsa wajen ganin ya shawo kan masu abokan sana’ar tasa, don ganin sun dawo sun cigaba da tafiyar Ganduje, amma da yawansu sun yanke kauna da cewa, matukar Afaka ne ke fada a ji, to za a cigaba da yaudarar su ne kawai.
Haka nan binciken ya cigaba da nuna cewa, hatta fitaccen mawakin nan, Aminu Ala, ya fice daga tafiyar Gwamna Ganduje ne sakamakon zargin da ya ke yi na cewa, bangaren Afakallahu ya yi ma sa yankan baya a tafiyar.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin shugaban hukumar tace finafinan, don ya kare kansa kan wadannan zarge-zarge, amma abin ya ci tura. Saidai idan hali ya yi, shi ma za mu zo da nasa bangaren.
A yanzu dai an ce, irinsu mashahurin Mawaki Ibrahim Ibrahim da fitacciyar Jaruma Rashida Maisa’a su na can su na ta fama da fafutukar hado kan ’yan Kannywood, don su dawo su cigaba da mara wa gwamnan baya a zaben cike gurbi da za a gudanar a jihar ranar Asabar 23 ga Maris, 2019.
©HausaLoaded
Post a Comment