Sharar Fage…

“A gaskiya kayan nan sun mi ki kyau Maryam sosai, lallai aiki ya same ni kenan.” “Aikin me?” Na katse shi da sauri cikin dariya, daidai inda ya cigaba da maganar sa da cewa, “Aikin saya maki kaya irin wannan kalar mana Maryam, saboda a gakiya kalar ta karbi jikinki kwarai da gaske.”

Ya yi shiru daidai inda ya sake kura min ido na ’yan mintuna sannan ya dora da, “Ni wannan kwalliya ta ki in ban da fita aiki ya zama dole, Allah da na yi zamana na cigaba da kallon ki abi na.” Dariya mai karfi na kece da ita, lokaci guda kuma na mike na dubi mijin nawa na ce, “mu je na raka ka wajen Babur dinka, kar ka makara aiki.”

Mun fito ne tsaye bakin falon mu mu ka ga Aisha kanwar mijna zaune. Na yi mamaki matuka da rashin sanin zuwanta, inda a nan ne ta ce ma na ta ma dade da zuwa. A tsat-tsaye su ka gaisa da yayan nata saboda ya na sauri zai makara aiki.

Na raka shi na dawo na same ta jikinta a sanyaye inda ta ke, na dube ta na ce ma ta, “lafiya dai ko Aisha?”
“Lafiya lau, wallahi Auntyna, kawai hirarku da yayana ce ta birge ni. Yadda ya ke yabon kwalliyarki abin sha’awa, sabanin mijina da kowacce irin kwalliya zan yi bai ma san Ina yi ba. Wallahi Aunty wannan abu ya na yi min ciwo ainun.”

Bin ta na yi da kallo ganin yadda gabadayan yanayinta ke nuna yadda ta ke jin takaicin abin a ranta.

Ginshiki

Maza kenan manya! ,Wannan matsalar ta rashin yabawa wajen maza, abu ne daya kwakwashi kaso mafi rinjaye cikin maza. Maza mafi yawanci wannan halin ko in kula din nasu na ci wa mata tuwo a kwarya sosai .Itace mace wata halitta ce mai son yabawa da nuna godiya, wanda in ta samu hakan ba wai kawai zata ji dadi a zuciyar ta ba ne kawai, a’a!, zata sake zage damtse ne wajen ganin ta sake yin abinda za’a yabe ta, a kuma gode mata ne. Amma abin mamaki Maza da daman su sam basu da wannan halin yabon ga matan su, wasu don rashin kulawa, wasu kuma don girman kai, wanda wani shirme maras tushe ke hawa kan su, ya sa musu tunanin wai in suna yabon mace da gode mata raini zai kawo, Wa ya fada muku haka maza, ai duk macen kwarai in taji mijin ta ya yabe ta, tare da godiya, wani girma da daraja zata kara ba shi fiye da tunani, sannan ta ji dadi a zuciyar ta tare da kara kaimin ganin ta cigaba da aikata abinda zai cigaba da yabon nata. Akwai Abubuwa da dama da ya dace namiji ya dinga yaba mata akai, abubuwa kamar:-

*Hakkin aure
Namiji ya sani ko kwanciyar aure yayi da matar sa, In ya gode mata bai fadi ba, sai ma kima da lada da zai samu.

*Kwalliya
Haka in mace tayi kwalliya, shima ya dace namiji ya nuna yaji dadi, har ma hada da “Kin yi min kyau sosai “.

*Kunshi
Matar ka kuwa na yin kumshi maza fara nuna kyan kumshi, tare da kama hannun ko kafar ka yaba kumshin yadda ya kamata.

*Kitso
Haka ma kitso da matar tayi, dacewa yayi ka shafa kitson ma wajen yaba kitson.

*Shamfo
In kuma shanfo ne shima hakan ya dace kayi.

*Girki
Girki kuwa kamata yayi kana ci ma kana santi tare da yabo da godiya.

*Gyaran gida
A yayin da in ka dawo daga aiki ka ga gida ya sha gyara tsaf, to maza fara kuranta matar ka tare da lafazan yabawa da godiya.

*Gyara yara
Haka yaran ku, akoyaushe ka dubi matar ka ka ga ta gyara muku yara, kar ka yi kasa a kwiwa wajen yaba mata tare da nuna farin cikin ka karara.

*Mutumta Iyaye, ’yan uwa, Abokai, Dangi, Makota
Haka in matar ka ta kyautatawa mahaifan ka, ko y’an uwan ka, ko abokai da sauran dangi maza cikin azama gode mata tare da bata kyakkyawan yabo da sa albarka.

A karshe maza kafin sa aya a alkalami na zan so in muku wani kira na Don Allah a dinga siyawa mata sutturar da zasu yi muku kwalliya, kudin kitso, kudin kumshi, na shamfo da duk sauran abubuwa da mace ka iya bukata don gyaran jikin ta, gwargwadon karfin ajjihun ka. Saboda akwai wasu mazan kuma a gefe guda da ke cewa matan su basa yi masu ire iren wannan kwalliyar, bayan kuma basa basu kudin yin kwalliyar, kila kuma matan basu da hanyar samun kudin ta ko’ina. 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top