Labari da dumi duminsa daga Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sake tabbatar da sake bullar cutar coronavirus (COVID-19) a jihar Legas.
Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a jihar Edo a ranar Litinin ya ce mara lafiyan Dan Najeriya ne kuma yana daya daga cikin Wanda sukai hulda da Dan asalin kasar Italiya Wanda ya shigo Najeriya dauke da kwayar cutar.
Ya bayyana cewa mara lafiyan , wanda yanzu a ka keɓance shi, yana karkashin kulawar likitoci.
Cutar dai ta bulla Najeriya ne a karan farko tun ranar 27 ga watan Fabrairu.
Wanda Kusan mutane 110,000 a duniya sun kamu da cutar kuma sama da 3,000, akasarinsu a China da Italiya sun mutu.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment