Ita dai tafarnuwa da citta an dauki lokaci mai tsawo ana amfani da su.Tun Kamin zakkuwar kimiya fiye da shekarru dari biyar da suka gabata,mutanen da suna amfani da tafarnuwa a matsayin maganin wasu rashin lafiyoyi masu dama.

A yayinda ita kuma citta (ginger) suka dauketa a matsayin kayan karawa abinci kamshi da armashi,alhali ashe magani ce ta musamman wanda tun kimanin shekarru fiye da dari da suka shude wasu suke amfani da ita a matsayin magani daga bisani ne kimiya ta zurfafa bincike akanta inda aka tarar da dimbin amfani a tareda citta.

To ganin kowace da irin rawar da take takawa wajen yaki da qwayoyin cuta da kuma inganta lafiya to sai aka dubi yiwuwar hadasu a waje daya wanda tuni aka tabbatar da za a iya hada citta da tafarnuwa a gauraya waje daya ayi amfani dasu zasu kasance wani magani mai karfin gaske.(Strong antibiotics
,anti viral da kuma anti fungal)
Ga kadan daga cikin maganin da hadin citta da tafarnuwa su ke yi :

1- Rashin jin dadin ciki ko kabewar ciki ko kumburinsa musamman idan anci abinci ko kuma mai fama da wannan matsalar a kullum.

2.Hauhawan jini da dasqarewar jini.

3.Gudawa.

4.Bayan gari mai tauri da jin zafi a yayin da aka je toilet ko jin ciwo a cikin dubura ba tareda akoi wani kurji a cikin duburarba.

5.Zafin ciki ko tusushin ciki da yawan sakin gas ko gyatsa mai wari.

6.Magani ne ga mafiyawan kwayoyin cuta a cikin ciki da hanji.

7.suna Bude hanyoyin jini wanda zai baiwa jini samun damar zagayawa a ko ina a cikin jiki (enhances proper blood circulation).

8.kara karfi da lafiya hadi da shawar jima’i.(enhances sexual activity).

9.Maganin kwayoyin cuta na bacteria da viruses da fungi.

10.Cutukkan tari da sanyin kirji da yawan atishewa da mura da kuma kaikayin makogwaro.

11.Tashin zuciya,yawan zubarda yawu ko taruwarsu a cikin baki,amai,kurajen baki da na makogwaro.

13.Zafin fitsari ko wani urinary tract infections a sabili da kwayar cutar Escherechia coli.

14.Yana sa cin abinci sosai ga mai fama da matsalar rashin iya cin abinci ya koshi (ensures appetite).

15.Ciwon jiki da ga6o6in jiki da kasala da yawan ciwon kai.

16.Rashin lafiyoyin da mutum ke tashi dasu da safe (morning sickness) kamar kumburin ciki,gyashin gyamba,tusa,kasala da ciwon jiki.

17.Maganin sanyin da ake dauka ta saduwa waton sexually transmitted diseases.


Yanda Ake Hadasu
– cup daya madaidaici na ruwa.
– Garin tafarnuwa kashi daya bisa uku na karamin cokali (5ml) tea spoonfull
garin citta shima kashi 1/3
– Sai a zuba su duka a tafasa a cikin ruwan zafi.idan ya huce za a iya tarfa zuma kadan sai a sha
ko kuma ka yayyanka tafarnuwa gunduwa gunduwa sai ka jefa a kofin ruwa haka itama citta sai ka jefa qwara daya ka gauraya ka tafasa.

– Haka kuma za a iya amfani da garin ga nama ko miya a zanka ci.




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top