Me baiwa shugaban kasa shawara kan shari’a kuma ministan shari’a na kasa,Abubakr Malami ya bayyana cewa bai san iya yawan kudin da tsohon shugaban kasa, Marigayi janar Sani Abacha ya sata ba.

 

Ya bayyana hakane a cikin wata wasika da ya mayarwa kungiyar kula da yanda ake gudanar da harkokin gwamnati ta SERAP data aika ma ofishinsa inda take neman bayani kan yawan kudin da Abacha ya sata da kuma abinda aka yi da kudin da aka kwato zuwa yanzu.

 

Malami yace daga hekarar 1999 zuwa 2015 an kwato Dala Biliya  5 na Abacha amma babu bayanin yanda aka yi amfani dasu.

 

Yace saidai wannan gwamnatin ta kwato Dala Miliyan 322 daga kasar Switzerland wanda kuma aka yi amfani dasu wajan shirye-shiryen inganta rayuwar ‘yan kasa da rage musu radadin talauci. Yace akwai kuma Dala miliyan 308 wanda aka kwato daga Island of Jersey wanda za’a yi amfani dasu wajan gina titunan Kano zuwa Abuja da Legas zuwa Ibadan da kuma Second Niger Bridge.

 

Saidai SERAP  ta hannun mataimakin daraktanta, Kolawale Oludare ta bayyana cewa bata gamsu da wannan bayani na gwamnatin tarayya ba dan haka zata maka ta a kotu bisa tanadin dokar yancin samun labarai data gayawa ‘yan Najeriya dalla-dalla yanda aka yi da kudin da Abachar ya sata da aka kwato.



© hutudole

Post a Comment

 
Top