Hukumar agajin gaggawa ta NEMA a Najeriya ta ce akalla mutum 15 suka mutu kuma da dama suka jikkata sakamakon fashewar bututun mai a Legas.
Babban jami’in hukumar NEMA Ibrahim Farinloye ya shaida wa BBC cewa sama da gidaje 50 ne suka kone a gobarar da ta soma a safiyar Lahadi.
Al’amarin ya faru ne a kusa da wata makarantar kwana da ‘yan mata. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an ceto yara 15.
Wakilin BBC a Legas ya ce jami’an kashe gobara a jihar sun shafe dare suna ta kai komo domin tabbatar da wutar da ta kama a Unguwar Abule Ado a yankin Festac ba ta tsallake ba an killace ta.
Kuma ya ce sama da mutum 300 aka samawa sansani a Igando bayan gobarar ta ci gidaje da shaguna da dama.
Zuwa yanzu ba a bayyana musabbabin gobarar ba, inda kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa BBC cewa wasu na ganin kamar man fetir ne wasu kuma na tunanin gas ne.
Fashewar bututun mai a Najeriya dai ba sabon abu ba ne, kuma hakan na faruwa ne sakamakon fashewa da satar danyen mai da ake yi.
© hutudole
Post a Comment