Aduwa Da Magungunanta (Balanites aegyptiaca)
Ga dukkanin alamu zaman birni ya yi tasiri ko bata wannan al’umma fiye da yadda ake zato. Ko shakka babu a wannan lokaci yara da dama ba su san mece ce aduwa ba, ballantana su san cewa tana da matukar amfani wajen lafiyar dan Adam. Baya ga shan aduwa da muke yi saboda dan zakin da take da shi, tana da kuma amfani a jikin bil Adama. Kadan daga cikin amfanin nata kamar yadda masana suka yi bincike a kai sun hada da, maganin shawara, tsutsar ciki, gyambon ciki, maganin tinjere, fyarfyadiya, ciwon asma, zawayi, attini da dai sauran su.
Ana samun bishiyar aduwa a kasashen Afrika da Indiya da wasu kasashen kudancin Asiya da kuma na Larabawa. Mutanen Habasha na kiran aduwa da Kudkuda, larabawa na kiran ta da Zachun, Indiya na kiran ta Enguwa ya yinda mutanen Swahili kuma na gabashin Afrika ke kiranta Mjunju.
Man Aduwa:
Idan aka matse kwallon aduwa, ana iya samun man girki da ya kai kashi 45 cikin dari, wannan mai na kwallon aduwa na da matukar amfani idan ana dafa abinci da shi. Yana kuma taimakawa wajen magance yawan Cholesterol da ke kawo toshewar hanyoyin jini da Asma da sauran cututtukan da muka ambata a baya.
Asma (Athma):
Ana iya nika kwallon aduwa a mayar da shi gari sai a rika dibar garin kimanin cokali goma ana zubawa a ruwa kimanin cikin kofi guda ana sha da safe har na tsawon kwanaki goma.
Tsutsar Ciki:
Haka zalika, a nan kuma busar da kwallon aduwa ake yi a daka shi har sai ya zama gari sannan a rika zubawa a kunun gero ana sha lokaci bayan lokaci. In Allah Ya so Ya yarda za a rabu da tsutsar cikin kowace iri ce da ke cikin hanjin mutum ko kuma yara.
Gyambo:
A bangaren masu fama da gyambo kuma, sai su samo ganyen aduwa dakakke ko kuma a daka shi a danyensa a rika wanke gyambon da shi, cikin dan kankanin lokaci insha Allahu gyambon zai kame ko ya bushe ba tare da wani bata lokaci ba.
Ciwon Fatar Jiki:
A nan kuma sai a samu man da aka fitar daga jikin ‘ya’yan aduwa a rika shafawa a jiki baki daya, yana maganin kurajen jiki sosai, kazalika yana maganin sanyin kashi.
Kamuwa Da Fitsarin Jini:
A kan daka bawon aduwa har sai ya zama gari, sannan a sanya a cikin ruwan da yara kan yi wanka da shi, misali kamar kududdufi domin kashe kwayoin da ke haddasa fitsarin jini da sauran wasu kwayoyin cututtuka irin su kurkunu da sauran su. Sai dai kuma wannan yana iya kashe kifaye da su dodon kodi da ke cikin ruwan ko kududdufin.
Tinjere (Syphilis):
Bayan an dafa bawon itacen aduwa, ana shan sa ne kadan-kadan don kuwa yana maganin cutar tinjere kwarai da gaske.
Kunburin Sawu Ko Na Jiki (Oedema):
Domin maganin wannan cuta ta kumburin sawu ko jiki, sai a dafa saiwar aduwa a cikin miya a rika sha.
Kazalika yana yin har maganin ciwon ciki.
“Ka tabbata ka tuntubi likitanka kafin ka fara yin amfani da kowane irin magani”.
© Sirrinrikemiji
Yaya adadin shan sa?
ReplyDelete