Dan wasan gaba na Super-Eagles, Odion Ighalo, ya bayyana yadda yake kunzige kudin abincinsa don kallon Manchester United tun yana yaro.
Ya fadi hakanne kafin wasansa na farko na Manchester.
Ighalo ya kasance mai kaunar Manchester United koyaushe. Lokacin da suka girma a Najeriya, Ighalo da ‘yan uwansa sun kasance manyan magoya bayan kungiyar, kuma suna ajiye kudinda za’a basu don cin abincin dare saboda zasu kalli kungiyar da suke so.
Ya bayyana cewa duk Wanda yasan shi lokacin da yana yaro yasan shi da goyan bayan Manchester United. kallan tashar kwallo sai kana da iko, Inji dan wasan inda ya kara da cewa kasancewar iyayen sa basu da ikon haka, yasa yake zuwa gidan kallo domin ya biya ya kuma kalli wasan.
© hutudole
Post a Comment