An samu fashewar wani abu a Abule Ado, wata unguwa a karamar hukumar Amuwo Odofin da ke jihar Legas a safiyar ranar Lahadi.
Yayin da har yanzu ba a san musabbabin fashewar ba, wani mazaunin garin Festac wanda ke kan iyaka da Abule Ado, ya ce mutane da yawa sun ji rauni, ya kuma shafi yankuna da dama ciki hadda makarantar kwana ta katolika ta mata.
“Wataƙila bututun mai ne ya fashe,” in ji shi.
An ji karar fashewar abin ne a garin Okota mai nisan kilomita 16, in ji wata majiya.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.