Wata babbar kotun jihar Kaduna wacce Mai shari’a Binta Zubairu ke jagoranta ta bayar da umarnin dakatar da gwamna Nasir El-Rufai da duk wani jami’in gwamnati daga rushe gidaje sama da 2,000 a garuruwan Nisi da Tasu na karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.
Daily trust ta rawaito cewa al’ummomin biyu suna da gidaje sama da 2,000 wadanda ke da adadin mutane sama da 10,000, majami’u 25 da makarantu 14.
Al’ummomin yankin Sun kai kara kotun ne ta hannun kungiyar lauyoyin da Sam Atung Esq ya jagoranta tare da neman kotu ta ba da umarnin dakatar da rushe musu gidaje.
Barrister Atung ya fadawa manema labarai jim kadan bayan an dage sauraren karar zuwa 30 ga Maris cewa wasu daga cikin gidajen suna da amincewar hukumomin gwamnati da suka dace a jihar, yana mai jaddada cewa daya daga cikin gidan a kauyen Nisi shi ma yana da Takaddun shaida na zama.
© hutudole
Post a Comment