A jiya ne tashar talabijin na jihar Kaduna (KSMC) ta fara watsa shirye-shiryen ta a bisa tsarin dijital.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya taya shugabannin tashar da ma’aikatan ta gaba daya murnar samun wannan ci gaba.
Malam El-Rufa’i ya kuma yi godiya ga shugabannin KSMC bisa rayar da gidan talabijin din zuwa wannan mataki.
Daga karshe ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta kuduri aniyar mayar da KSMC tasha mai watsa shirye-shiryenta a duniya.
© hutudole
Post a Comment