Shafin premium times hausa ya Wallafa, Sakamakon wani bincike da masana suka yi ya nuna cewa manoma sun fi ma’aikata da ke aiki a wasu fannoni na rayuwa kuzari da himma a wajen saduwa da iyali.

Likita Kate Moyle da ta kware wajen nazarin harkar jima’i kuma mazauniyar kasar Amurka ta bayyana sakamakon wani bincike da aka yi game da kwazon mazaje a wajen saduwa da mata.

Kate tayi bincike ne akan wasu maza masu yawa, mazauna kasar Amurka da Britaniya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa akalla kashi 67 bisa 100 na manoma sukan sadu da mace akalla sau daya a rana. Kashi 21 ma magina kuma kan sadu da mace akalla sau biyu ne a mako. Kashi 17 bisa 100 cikin wannan adadi masu gyaran gashi ne sukam sukan sadu da mace sau daya ne duk mako.

Sannnan kuma binciken ya nuna cewa lauyoyi sun fi kowa shirga karyar suna jin dadi a lokacin saduwa da mace.

Malalata cikin wadannan rukunin da aka yi bincike akai sune ma’aikatan gidajen yada labarai wadda aka gano cewa mafi yawa daga cikin su sau daya tal ne suke iya saduwa da mace a wata.

“ Manoma na motsa jikinsu a ko wani lokaci. A dalilin haka ne yasa idan suka kwanta da mace sai ta yaba, ba kaman yadda wasu da ba manoma ba. Haka kuma su kansu matan da muka zanta da su sun musamman wanda mazajen su manoma ne sun tabbatar da cewa akwai su da kwazo a wajen jima’i.

Likita kate ta kara da cewa duk da cewa mutane da dama na gudun aikin noma saboda wahalar sa da kuma yawan motsa jiki, bincike yanuna cewa an fi samun lafiya idan ana aikin noma domin ana motsa jiki matuka. Hakan yana kara wa mutum lafiya da tabuka abin abin azo a agani idan ya kwanta da matar sa.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top