Da ba dan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya baki akan rikicin dake tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Sarkin Kano, Sanusi Muhammadu Sanusi II, gwamnan jihar ya riga ya kammala shirin sa na cire Sarkin tun a shekarar 2017, kamar yadda wata majiya dake da kusanci da gidan gwamnatin jihar ta sanarwa da Daily Trust jiya a Abuja.
Daily Trust ta ruwaito bayani akan zargin da ake yiwa fadar shugaban akan cewa da hannunta a tsige Sarkin daga kujerarshi, majiyar ta ce fadar shugaban kasar tayi iya bakin kokarinta wajen ganin wannan lamari bai faru ba.
Majiyar ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kokarin sasanta tsakaninsu, inda har ya bayyana cewa matukar lamarin ya nemi wuce gona da iri to ba zai yi kasa a guiwa ba wajen sanya dokar ta baci a Kano ba.
Sarkin dai ya harzuka gwamnan jihar ne bayan ya kalubalanci gwamnatin jihar akan kudin aikin hanyar jirgi da gwamnatin jihar ta fitar a watan Afrilun shekarar 2017.
Mutumin da yayi magana da Daily Trust ya nemi a sakaye sunanshi, ya ce a lokacin da Ganduje ya gama shirin tsige Sarkin a shekarar 2017, ya nemi shawarar shugaba Buhari, inda shugaban kasar ya ce kada ya cire shi saboda hakan bai kamata ba.
“Wannan ya zo ne a wata takarda da shugaban kasa ya aikowa da gwamnan a ranar 17 ga watan Nuwambar shekarar 2017, inda take bayani akan shawarar shugaban kasar. Shugaban kasar ya bukaci Abba Kyari da yabi hanya mafi dacewa domin daidaita tsakaninsu,” cewar majiyar.
Ya ce hakan ya sanya aka kirkiri kwamiti ta gwamnoni guda biyar, wacce gwamnan Ekiti Dr. Kayode Fayemi ya jagoranta, wadanda suka yi iya yinsu domin tabbatar da daidaito tsakaninsu, inda a lokacin ne gwamnan kuma ya sake hawa kujerar gwamnan jihar a karo na biyu a shekarar 2019.
Ya ce gwamna Fayemi, da gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru da shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa sun kai ziyara jihar ta Kano domin shawo kan lamarin gwamnan da Sarkin, duka kuma anyi hakane domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
A cewar shi, gwamna Ganduje ya bayar da ka’idoji akan wanzar da zaman lafiyarsu, inda yace Sarki Sanusi ya janye kararrakin da ya shigar kotu akan gwamnatin jihar, kuma Sanusi ya amince zai janye wasu daga cikin kararrakin, amma kuma yaki yadda ya janye wasu.
Majiyar ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana matukar girmama Sarki Sanusi saboda haka babu yadda za ayi ya sanya Ganduje ya cire shi.
© hutudole
Post a Comment