Rundunar ‘yan sanda ta jihar Yobe a ranar Asabar ta bukaci jama’ar jihar da su yi taka-tsantsan tare da bayar da bayanan da za su taimaka wajen dakile hare-haren kungiyar Boko Haram.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Dungus Abdulkarim.
 Rundunar ta yi bayanin cewa kiran nata ya mayar da martani ne ga sabbin hare-hare da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi, wanda harin ya faru a garin Dapchi a ranar Laraba da ta gabata.
Rundunar ta yin Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai kan hedikwatar’ yan sanda da ke Dapchi.
 Sanarwar ta tabbatar da cewa Kwamishinan ‘yan sanda Yahaya Abubakar, ya ziyarci Dapchi ranar Juma’a don nuna juyayi kan kashe-kashen da aka yi kwanan nan.
Abun dubawa anan shine Kungiyar Boko Haram da kungiyar ISIS a yammacin Afirka, ISWAP, sun tsaurara hare-hare a cikin ‘yan watannin nan.


© hutudole

Post a Comment

 
Top