Kungiyar Liverpool ta lallasa AFC Bournemouth da ci 2-1 a wasan da suka buga na ranar Asabar inda Bournemouth ce ta fara cin kwallo mintuna 9 kacal da take wasa amma Mohamed Salah da Sadio Mane suka farke kwallon suka kuma kara.

 

Saidai da kyar liverpool ta sha a wasan dan kuma Bournemouth ta so ta kara mata kwallo wadda shiga raga kawai zata shiga dan ta tsallake gola amma James Milner ta fitar da ita, ya sha yabo sosai kan wannan bajinta.

 

 

Da wannan nasara,Liverpool ta yi nasara a karin farko tun bayan rashin nasara da ta jera wasanni 3 tana yi a baya.

 

Kwallon da Mohammed Salah yaci itace kwallonshi ta 80 a wasa na 100 da ya buga a gasar Premier League sannan kuma ya zama dan kwallon Liverpool na farko tun Michael Owen a kakar 2002-03 da ya jera kakar wasanni 3 yana kwallaye akala 20.

 

 



© hutudole

Post a Comment

 
Top