A ranar Lahadin da ta gabata Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ba da sanarwar cewa, an gano wasu mutane 23 da ake zargi da cutar Coronavirus (COVID-19) a wasu jihohin.

 

Jihohin Su ne Edo, Legas, Ogun, Kano da Abuja, Babban Birnin Tarayya (FCT).

 

Hukumar NCDC ta ce har zuwa yanzu mutum daya ne aka tabbatar ya kamu da cutar.

 

Darakta Janar na NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu, shine ya bayyana haka a wata hira da yayi da NAN ranar Lahadi a Abuja.

 

Ihekweazu ya ce an gano mutum 219 da suka yi mu’amala da wanda ake zargin na dauke da cutar, wanda suka hada da Otel, wajan aiki da kuma ma’aikatan lafiya.

 

A cewar sa har zuwa yanzu babu wani rahoto da aka sake samu na bullar cutar.



© Abubakar Saddiq

Post a Comment

 
Top