Wani abu da yake ban takaici shi ne; idan 'Yan Hakika sun zagi Annabi (saw) sai ka ga jagororin Dariqa - Shehunansu da Furofesosinsu da Daktocinsu da tsagerun matasansu - sun fito suna ta kumfar baki, da sunan kare Annabi (saw), alhali a bisa hakika Dariqar kawai suke karewa da Shehunanta. In ba haka ba, Wallahi babu wanda zai yaki Hakika alhali yana cikin Dariqa. Saboda hakikar nan ita ce kololuwar Maqami a cikin Sufanci.

Bayan haka, su wadannan Shehunai da ake zagin Annabi (saw) a kansu, wato Shehu Tijjani da Ibrahim Inyas, su ne suka bai wa kawunansu matsayi da Siffofin Allah, suka fifita kawunansu a kan Annabawa da Manzanni a cikin littatafansu, kuma kullum ana karanta wadannan littatafan ga Muridai. To ta yaya Muridi ba zai fahimci ana nuna masa cewa; ya allantar da Tijjani ko Inyas ba?!

Tijjaniy da Inyas su suka fara bai wa kawunansu Maqamai na allantar da su.
Shehu Tijjaniy ya ce:
وما أحد من أوليا الله كلهم *** يسكّن صحبه أعالي جنة
بغير الحساب والعقاب سوى أنا *** ولو فعلوا في الذنب كل جريمة

Ibrahim Inyas ya ce:
ومن يحبني ومن يراني *** في جنة الخلد بلا بهتان

Kuma ya ce:
إن قلت كُنْ يَكُنُ بلا تسويفي *** قد خصّني بالعلم والتصريفي

Yanzu ka duba irin wadannan munanan maganganu fa!
Ka ga kowannensu ya bai wa kansa Maqami da matsayin Allah, kuma sun halasta wa mabiyansu aikata kowace irin jarima da alfasha da laifi, da sunan sun lamunce musu Aljanna.

Saboda haka duk jagora a Dariqan da yake babatu -wai- 'Yan Hakika sun zagi Annabi (saw) ba da gaske yake yi ba. In har da gaske yake yi kafin ya kafirta 'Yan Hakika to dole sai ya fara kafirta Tijjani da Inyas, saboda su suka fara kai kawunansu wannan Maqami, suka ba wa kawunansu wadannan matsayi, suka allantar da kawunansu kafin Muridansu. A je a duba littatafansu a gani.
Wai tsabtace Sufanci!
A dauri kashi ko a bata igiya?!

Allah Ka tsare mana imanin mu Amin

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top