Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra(IPOB) ya yiwa tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma tsohon hafsan soji, Janar Theophilus Danjuma, ihu bisa ga kiran da suke yi na sake fasalin kasar.
Janar Yakubu Gowon (retd), wanda ya halarci wani taro wanda Gidauniyar Shugabanci ta Igbo ta shirya a ranar Alhamis, ya yarda cewa an bar ƙabilar Igbo a baya a siyasar Nijeriya.
Ya ce, “Na yi imani da cewa an yi wa Igbo rashin dai dai, batun tsarin mulki ya kama a magance shi tare da samun daidai to, da kuma dawo da kwarin gwiwa ga kowa.
Haka Shima Obasanjo ya yi Allah wadai da halin da ake ciki a kasar nan a cikin jawabin da ya yi a ranar Asabar a bikin gabatarwa na tunawa da Frederick Fasehun.
Nnamdi Kanu, ya bayyana cewa, yayi imani da cewa wadannan mutane su ne suka yaki Igbo fiye da sake gina kasar a Shekarar 1967, ya kuma bayyana yadda a lokacin aka hade musu kai aka yaki Biafra, Wanda suka Amince da sake fasalin kasa.
© Abubakar Saddiq
Post a Comment