Raliya Muhammad matashiyar jaruma ce kuma furodusa a Masana’antar Kannywood da yanzu take haskawa. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana yadda ta shigo masana’antar da yadda ta dauki nauyin fim dinta na farko, mai suna Raliya da nasarorin da ta samu da burin da take da shi a masana’antar:

Mene ne tarininki a takaice?

Da farko dai sunana Raliya Muhammad. An haife a Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna. A can na yi karatun firamare, na yi karamar sakandare. Daga nan kuma na koma Jihar Zamfara, inda na karasa karatuna na sakandare a can a shekarar 2014. Kuma na yi karatun Difloma a bangaren Tsabtar Muhalli a Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Tsafe a Jihar Zamfara, inda na kammala a shekarar 2018.

Yaya aka yi kika tsinci kanki a masana’antar shirya fina-finai ta Hausa?

Na shigo masana’antar ce ta hannun yayana, wanda shi kuma mawaki ne a masana’antar da ya dade. Sannan kuma, dama can na dade ina sha’awar shiga harkar, amma kasancewa ina karatu, sai na dan danne sha’awar tawa.




Da na kammala karatuna, sai na nemi izini wajen iyayena cewa zan fara harkar fim da na dade ina sha’awa, kuma suka amince min. Sai na yi magana da yayan nawa, ya hada ni da masu bangaren da nake sha’awa, tun daga nan, abin sai godiya ga Allah, domin kullum kara ganin haske nake yi.

Yaushe kika fara harkar?

Kamar yadda na fada, sai da na kammala karatun Difloma na shiga harkar gadan-gadan, yanzu kimanin shekara daya da watanni ke nan.

Kin shigo ba da dadewa ba, amma har kin dauki fim dinki, sannan kin fito a jaruma a wasu fina-finai, wane bangare kika fi so a harkar?

Eh, to a gaskiya daukar nauyi fim na fara a farkon shigowata masana’antar, amma kuma ni na ja fim din da kaina.

Amma kuma gaskiya na fi ganin kaina a matsayin jaruma, duk da cewa na dauki nauyin fim, kuma zan ci gaba da daukar nauyin fina-finai a nan gaba.

Wane ne ubangidanki a harkar fim a yanzu?

To gaskiya, zan iya cewa El-Mu’az ne ubangidana a Masana’antar Kannywood. Shi ne mutum na farko da aka hada ni da shi lokacin da na shiga masana’antar kuma ya ba ni dukkan goyon bayan da nake bukata, kuma yana kan ba ni.

Daga baya kuma na samu goyon baya da karfin gwiwa daga dukkan wadanda na yi aiki da su, musamman manyan. Don haka zan iya cewa su ma iyayen gidana ne domin sun ba ni hadin kai kuma sun taimaka min sosai wajen ganin aikina ya yi kyau. Don haka ina matukar alfahari da dukkansu a wannan harka ta fim da ma rayuwata.



Fim nawa kika yi zuwa yanzu, kuma fim nawa kika fito?

A cikin wannan dan lokaci da na fada maka, na fito a manyan fina-finai uku. Daya daga ciki mai suna Raliya nawa ne. Ni na dauki nauyinsa, kuma sunana ne ma aka sa wa fim din. Sai wadanda na hau akwai Sanata da Ranar Sallah. Yanzu haka kuma akwai wasu fina-finai da muke yin aikinsu da kuma wadanda ake shirin yinsu da yardar Allah.

Ganin kin dauki nauyin fim, kina kuma fitowa a jaruma, akwai bangaren da mata ba su cika shiga ba wato bada umarni, ko kina da sha’awar zama darakta nan gaba?

Kwarai kuwa, da yardar Allah nan gaba ina da burin zama darakta. Na fara ne dai da daukar nauyi da kuma jaruma da na fi sha’awa. Amma nan gaba ina so na zama darakta. Ina da burin haka.

Mene ne burinki a harkar fim?

Burina shi ne in bada tawa gudunmawar ga al’umma wajen ilimantarwa da nishadantar da su da fadakar da su. Sannan na dauki harkar fim a matsayin sana’a. Burina in zama fitacciyar jaruma a Najeriya baki daya, har sunana ya kai kasashen waje. Ina rokon Allah Ya sa mana hannu mu daukaka baki dayanmu.

Yanzu kina ganin burinki ya fara cika?

Kwarai da gaske burina ya fara cika. Yanzu ga shi na fara, kuma ya shiga kasuwa mutane sun kalla kuma sun yi na’am. Kuma a kullum ina samun sakonni daga masoya, inda suke nuna jin dadi a kan aikinmu tare da kara karfafa mana gwiwa. To ai sai godiya ga Allah kawai, da kuma addu’ar Allah Ya kara mana daukaka, domin gaskiya zan iya cewa na fara da sa’a, domin ina ganin haske.

Wane bangare kika fi sha’awa a sanya ki a fim?

Kowane bangare aka sanya ni, nakan yi bakin kokarina in bayar da abin da ake bukata a matsayina ta jaruma. Kuma a duk lokacin da na taka wata rawa a duk abin da aka sa ni, ana sam barka da aikin da na yi. Don haka muna fara da kafar dama, kuma kyan jaruma ta iya taka rawa a duk inda aka sanya ta, ko kuma duk matsayin da darakta ya ba ta. Kuma gaskiya duk matsayin da na fito yana burge ni.



Mene ne kiranki ga masoya?

Alhamdulillahi. Ina matukar godiya ga masoyana maza da mata bisa yadda suke nuna min kauna. Suna matukar kokari wajen karfafa min gwiwa ta hanyar kira a waya da kafofin sadarwa na Instagram. Sannan ina farin cikin sanar da su cewa kofata a bude take domin karbar shawara, ko gyara in sun ga kuskure a cikin aikina domin don su muke yin komai, don haka jin dadinsu shi ne jin dadinmu. Kuma a shirye nake in karbi gyara a duk lokaci da ya dace. Shafina ne Instagram shi ne rreal_ raliya, mai rr biyu, tsohon na real_raliya ya lalace.

Kina da wani kira ga manyan cikin masana’antar?

To a gaskiya kirana ga manyan masana’antar bai wuce su ci gaba da sa ido a cikin sana’ar wajen tabbatar da kowa yana tafiyar da aikinsa yadda ya kamata ba. Ya kamata manya su tabbatar da dokokin masana’antar suna aiki kuma suna da karfi a kan dukkan jaruman masa’antar, domin masana’antar wajen sana’a ce ba wajen wasa ba. Mun san suna kokari, amma su kara. Kuma su hada kansu domin ciyar da masa’antar gaba. Sannan su rika taimakon na kasa da su. Allah Ya kara sa mana hannu a cikin al’amuran masana’antarmu da albarka mai dorewa.

Wane kira za ki yi ga gwamnati kan masana’antar?

Da farko zan fara ne da yi kasata Najeriya addu’ar Allah Ya kara mata albarka. Ina rokon gwamnati duk da cewa mun san tana kokari, ta kara kaimi wajen taimakon matasa maza da mata domin samun aikin yi da za su dogaro da kansu. Wadanda ba su yi karatu ba ma a taimaka musu da sana’o’in hannu.

Ya kamata gwamnati ta karfafa mana gwiwa tare da tallafa mana, domin harkar fim akwai matasa da yawa a cikinta da ke cin abinci.



Sannan ina kara addu’ar Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya.

Akwai wata jaruma da kike koyi da ita a masana’antar fim baki daya?

Gaskiya babu kwaya daya tal da zan fitar domin dukkansu suna burge ni matuka. Kuma dukkansu ina koya daga gare su. Burina wata rana in zama babba kuma fitacciyar jaruma kamarsu. Shi ya sa na ce kowane bangare aka ba ni, zan yi a fim matukar bai saba ka’ida ba. Hakan zai sa in zama cikakkiyar jaruma. Kuma burina shi ne a ce duk fim da na yi, idan na fito mutane su kaunace shi, su yaba da aikin.

Kina da burin shiga fina-finan Kudu nan gaba?

Eh, ina da burin haka in Allah Ya yarda a nan gaba. Wannan ne ya sa ma nake da burin komawa makaranta domin in karanta bangaren fim wato Theater Art domin samun karin ilimi da haske a kan harkar don wata rana in kasance daga cikin jaruman da ake alfahari da su a duk Najeriya.

Me za ki ce kan rikice-rikicen da ake yi tsakanin jarumai a Masana’antar Kannywood?

Abin da zan ce shi ne mu rika hakuri da juna, domin lokuta da dama sabanin fahimta ne ke kawo haka. An zo an ce wani ya ce kaza a kanka, watakila ba ka yi bincike ba ko shi wanda ya fadi maka shi me ya ce, kawai ka bari zuciyarka ta baci Shaidan ya rinjaye ka ka aikata abin da za a dawo ana da-na-sani. To don Allah mu rika hakuri da juna mu kuma rika yi wa juna uzuri.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top