‘Yan sanda a paraguay sun kama tsohon dan wasan kwallon kafan Brazil Ronaldinho bisa zargin shiga kasar da fasfo na bogi.

‘Yan sanda sun binciki wani otal a Asuncion, babban birnin kasar ranar Laraba, inda tsohon dan wasan ya zauna da kaninsa.

Ministan harkokin cikin gidan Paraguay ya shaida wa ESPN cewa ana binciken Ronaldinho da kanin nasa amma ba a kama su ba.

Minista Euclides Acevedo ya ce sun musanta zargin da ake masu kuma suna bai wa hukumomi hadin kai.

A watan Yulin 2019, rahotan sun bayyana cewa an kwace fasfo din dan wasan na kasashen Brazil da Sufaniya bisa laifin kin biyan haraji.



© hutudole

Post a Comment

 
Top