Kamfanin Facebook Ya rufe wasu ofishoshin sa dake Landan da wani bangare a singapore, domin tambatar da kare lafiyar ma’aikatan sa,

Matakin ya biyo bayan samun daya daga cikin ma’aikan kamfanin da ya kamu da cutar COVID 19. wanda ke aiki a ofishin su dake Singapore.
Inda tuni Kamfanin ya dauki matakin rufe ofishoshin da lamarain ya shafa, a yayin da kamfanin ya umarci ma’aikatan sa da suna gudar da aikin su a gida har nan da zuwa 13 ga watan March.
A cewar wani mai magana, ya bayyana cewa Ma’aikacin da ke dauke da cutar ya ziyarci ofishin kamfanin dake Landan a ranar 24 zuwa 26, dan haka yasa kamfanin ya kulle ofishin domin tsaftacewa har zuwa ranar Litinin.
tun bayyan bullar cutar kamfanin na Facebook ya rurrufe wasu ofishoshinsa da dama domin tambatar da kare lafiyar ma’aikatan sa. Inda aka umarce su da yin aikin su a gida.


© hutudole

Post a Comment

 
Top