Wani matashi mai kimanin shekaru 19 Rafiu Adelena an kamashi da yiwa  Mai shekaru 52 da haihuwa fyade.

Lamarin ya faru a ranar 1 ga watan Maris 2020 a unguwar Ilesan Remo dake Jahar Ogun.
An rawaito cewa Matashin na zaunane da iyayansa haya a gidan matar da yayiwa fyade, bayan afkuwar lamarin an  mika shi ga hannun yan sanda, a inda ya  bayyana yadda ya aikata mummunan aikin, inda ya kada baki yace, Yayi amfani da maganin bacci da babarsa take a jiye dashi a cikin daki, sannan ya sanya a cikin abinci a lokacin da matar taci abincin sai bacci ya kamata anan ne yasamu Nasarar aikata son zuciyarsa a cewar Rafiu.
Bayan da hukamar yan sanda ta gayyaci mahaifiyar matashin, ta bayyana dalilinta na amfani da maganin bacci, inda tace takan kasa yin bacci wannan ne yasa take shan maganin.
A karshe hukumar yan sanda ta tabbatar da zata ci gaba da bincike kafin gurfanar dashi zuwa kotu, a inda ake zarginshi da laifin fyade.


© hutudole

Post a Comment

 
Top