Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Adams Oshiomhole ya daukaka kara bayan hukuncin wata kotu da ya sauke shi daga mukaminsa a ranar Laraba.
Mai magana da yawun shugaban Simon Ebegbulem ne ya bayyana hakan, inda ya ce sun nemi kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin.
“Kasancewar batun a gaban kotun daukaka kara, har yanzu Adams Oshiomhole ne shugaban jam’iyyar APC na kasa,” in ji Ebegbulem a wata sanarwa da ya aike wa BBC.
Tun farko dai Mai Shari’a Danlami Senchi ne na wata kotu a Abuja ya yanke hukuncin bayan karar da aka shigar cewa tuni aka dakatar da Mista Oshiomhole daga jam’iyyar APC a jiharsa ta Edo.
Wani mai suna Oluwale Afolabi ne ya shigar da karar.
Mista Afolabi ya fada wa kotun cewa tun da reshen APC na jihar Edo ya dakatar da Mr Oshiomhole daga jam’iyyar ranar 16 ga watan Janairu, bai kalubalanci dakatarwar ba lamarin da ke nufin ba shi da ja ga hukuncin jam’iyyar.
Cikin hukuncinta, kotun ta hana Mista Oshiomhole kiran kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Kazalika ta hana jam’iyyar kiransa a matsayin shugabanta, sannan ta yi umarni da kada a bar shi ya shiga ofishin APC.
© hutudole
Post a Comment